Najeriya: Jami'an tsaro sun hallaka 'yan bindiga 14 a Legas
Gamayyar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojin ruwa a birnin Lagos a kudancin Najeriya, sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga 14 daga cikin wadanda suka kutsa kai cikin wata makaranta a Igbonla, Epe da ke birnin na Lagos tare da sace wasu dalibai kanana guda 6, a ranar Alhamis din da ta gabata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An dai sace yaran ne daga wuraren kwanansu da misalin karfe 6 na safiyar ranar ta Alhamis.
Kafin sace yaran dai, sau uku, ‘yan bindigar suna hankoron idda nufinsu, wanda basu cimma nasara ba, sakamakon jami;an da aka girke suna tsaron makarantar.
Daga bisani ne suka huda katangar makaranta ta baya, inda suka yi amfani da shi wajen awon gaba da yaran.
Rahotanni sun ce gamayyar jami’an tsaron na cigaba da dannawa cikin jejin da ‘yan bindigar suka boye yaran domin ceto su, kuma a kokarin haka ne suka samu nasarar hallaka 14 daga ciki tare da kuma raunata wasu da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu