rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojan Najeriya Sun Fasa Garken 'Yan Boko Haram A Mokwa, Jihar Neja.

media
Babban Hafsan Sojan Najeriya Tukur Buratai AFP PHOTO/STRINGER

Sojan Najeriya na Brigade na 31 sun kai wani samame makwancin wasu da ake ganin take-takensu irin na 'yan kungiyar Boko Haram ne a mabuyarsu dake garin Mokwa a jihar Neja.

 


Bayanai na cewa an kai samamen ne bayan samun bayanan sirri, kuma har an kama wasu mutane uku da ake kyautata zaton jagororin kungiyar ce.

Birgediya Sani Usman Kukasheka, Daraktan Sojan Najeriya ya fadi cikin wata sanarwa cewa mutanen uku sun hada da Mustapha Mohammed da aka fi sani da suna Adam Bitri da kuma Ali Saleh da kuma Uba Mohammed.

A cewar sanarwar shi Mustapha Mohammed na daga cikin wadanda ake zargi da sace marigayi Dr Shettima Ali Mongono a shekara ta 2013.