Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Najeriya ta amince da dokar Rashawa

Majalsiar Dattawan Najeriya ta kada kuri’ar amincewa da dokar yaki da cin hanci da rashawa da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar mata a farkon shekarar 2016.

Majalisar Dattijen Najeriya ta amince da dokar Rashawa
Majalisar Dattijen Najeriya ta amince da dokar Rashawa venturesafrica
Talla

Dokar ta kunshi hadin kai da kasashen duniya wajen karbo dukiyar da ‘yan kasar suka sace suka jibge a can.

Kana akwai taimakawa wajen gudanar da binciken kan wadanda ake zargi da kuma karbo shaida dan hukunta su.

Dokar ta kuma kunshi mallakawa gwamnati irin kudaden da aka kwato na sata bayan kotu ta kammala shari’a.

An dai shafe sama da shekara guda kafin Majalisar ta amince da dokar, Yayin da kungiyoyin da ke yaki da Rasahwa suka jimma suna korafin kin hukunta wadanda ake cewa an samu da wawushe dukiyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.