rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM Maiduguri

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 11 suka mutu a harin Maiduguri

media
Nigerian soldiers in Maiduguri, Borno State on 25 March 2016. Photo: Stefan Heunis

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce akalla mutane 11 suka mutu a hare-haren da ‘Yan Boko Haram suka kaddamar a jiya laraba a garin Maiduguri


Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Borno Damian Chukwu ya ce an harbe mayakan na Boko Haram guda uku da suka yi yunkurin kai harin kunar bakin wake a maiduguri.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe daukacin mayakan na Boko Haram da su ka kaddamar da hare-haren a unguwar jiddari Polo a Maiduguri.

Daraktan yada labaran sojin kasar, Brigadier Janar Sani Usman Kukasheka ya ce da farko mazauna yankin sun shirya tserewa daga gidajensu amma yanzu komai ya lafa.

Janar Kukakasheka ya kuma tabbatar da karfafa tsaurara matakan tsaro tare da kara dakaru a yankin don hana barazanar irin wannan hari na bazata a nan gaba.

Rahotanni sun ce sama da mutane 20 suka jikkata a harin.

Harin na daren jiya ya kasance irinsa na farko da mayakan Boko Haram ke kai wa tun bayan karbe ikon wasu yankunan da ke karkashinsu.