rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Biafra Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Bamu da shirin kwashe 'yan kabilar Igbo daga arewa - Umahi

media
Wasu masu fafutukar neman kafa kasar Biafra a garin Aba da ke kudancin Najeriya. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI

Kungiyar Gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya, ta karyata rahotannin da ke cewa, gwamnonin jihohin yankin, sun gudanar da taro, don shirya yadda zasu samar da kudi da kuma ababen hawa, da za’a yi amfani da su wajen kwashe ‘yan kabilar Igbo daga arewacin kasar.


Shugaban kungiyar gwamnonin na kudu maso gabashin Najeriya, kuma gwamnan jihar Ebonyi, Mista David Umahi, ya musanta rahotannin, bayan taron a madadin gwamnonin jihohin yankin.

Umahi, ya bukaci, ‘yan kabilar Igbo da ke jihohin arewacin kasar, su cigaba da gudanar da harkokinsu nay au da kullum, tare da jaddada goyon bayan cigaba da zaman Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa.

Gwamnan jihar ta Ebonyi, ya kara da cewa baki dayan gwamnatocin yankin, suna aiki da jami’an tsaro, don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar ‘yan arewacin kasar da ke zaune a can, da kuma tabbatar da cewa ba’a bai wa bata gari damar tada zaune tsaye ba.