rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Boko Haram ta Fitar Da Bidiyo Cewa Sun Yi Nasara a Harin Maiduguri

media
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a tsakiya RFI

A Najeriya, mutumin nan dake cewa shine Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram ya fitar da wani sabon sakon Video inda yake cewa harin da suka kai garin Maiduguri Alhamis data gabata, sun cimma burinsu.


A sakon Bidiyon ya bayyana cewa za su yi amfani da makaman da suka kwace daga sojoji da suka tsere domin kai wasu hare-hare.

‘Yan sanda da bangaren Sojojin Najeriya cikin sanarwa da suka bayar Juma’a  data gabata sun bayyana cewa sun yi nasarar murkushe ‘yan Boko Haram da suka kai hari garin Maiduguri ranar Alhamis.

Sabon Bidiyon na mintoci 23 an fitar dashi ne cikin kafar sadarwa ta YouTube.