rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya: An kame madugun kungiyoyin sata da garkuwa da mutane

media
Mutumin da rundunar 'yan sandan Najeriya ta shafe tsawon lokaci tana nemansa ruwa a jallo, saboda rawar da ya dade yana takawa, wajen shugabantar wasu gungun masu sata da garkuwa da mutane. The Nation Nigeria

Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta samu nasarar kama wani kasurgumin mai sata da kuma garkuwa da mutane a birnin Legas, bayan shafe lokaci mai tsawo tana nemansa ruwa a jallo.


Shugaban rundunar yan sandan ta musamman da aka fi sani da IRT, ACP Abba Kyari, ya shaidawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa, mai laifin da ke amsa sunan Evans, wanda suka shafe tsawon lokaci suna nema ruwa a jallo, sun damke shi ne, a wani gidansa da ke Magodo a birnin Legas.

ACP Kyari, yace, mutumin ya kwashe akalla shekaru 7 yana shugabantar gungun masu sata da garkuwa da mutane daban daban, wadanda sukai nasarar amshewa mutane da dama biliyoyin nairori kafin sakin wadanda suka sace.