Isa ga babban shafi
Najeriya

Osinbajo ya sanya hannu kan kasafin kudin Najeriya

Mukaddashin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2017 don zama doka.

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo
Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo
Talla

Mr. Osinbajo ya rattaba hannun ne da misalin karfe 4.40 na yammacin ranar Litinin agogon kasar, kuma a gaban shugaban ma’aikata a fadar gwamnnatin kasar, Abba Kyari da shugaban Majalisar Dattawan kasar, Bukola Saraki da Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da kuma Ministoci da manyan jami’an gwamnatin kasar.

Osinbajo ya ce, sanya hannun da ya yi na da matukar muhimmanci dangane da aiwatar da shirin habbaka tattalin arikin kasar da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a cikin watan Aprilun da ya gabata.

Kasafin kudin na dauke da jumullar Naira tiriliyan 7.44.

A ranar 10 ga watan jiya ne Majalisar Dattawan ta zartar da kudirin kasafin kudin bayan an kara kudin da ke kunshe a cikinsa daga Naira tiriliyan 7.28 da shugaba Buhari ya gabatar a cikin watan Disamban bara zuwa Naira tiriliyan 7.44.

Sanya hannu kan kasafin na zuwa ne a yayin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ke duba lafiyarsa a birnin London.

A karon farko kenan cikin shekaru na baya-bayan da wani mukaddashin shugaban kasa a Najeriya ya sanya hannu kan kasafin kudin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.