rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EFCC na binciken Yakubu Dogara kan kasafin Najeriya

media
Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Yakubu Dogara

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC na binciken shugaban Majalisar Wakilan kasar, Yakubu Dogara bisa zargin sa da kara wasu alkaluma a kasafin kudin shekarar 2016 ba bisa ka’ida ba.


Wata takardar wasika da Kamfanin Dillancin Labaran Reuters ya gani wadda aka rubuta a ranar 9 ga watan Yuni, ta nuna cewa Mr. Dogara ya kara alkaluman ne bayan Majalisa ta amince da kasafin kudin.

Kawo yanzu dai mai magana da yawun Dogara bai mayar da martani ba dangane da wannan rahoton duk da kiran sa da manema labarai suka yi ta wayar tarho.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari da ke duba lafiyarsa a birnin London ya yi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa da ke ci gaba da haifar da koma-baya ga Najeriya.