rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojan Najeriya Sun Kama Wani Jagoran Boko Haram

media
Babban Hafsan Sojan Najeriya Tukur Buratai AFP PHOTO/STRINGER

Rundunar sojan Najeriya ta sanar da cewa ta kama wani kasaitaccen dan kungiyar Boko Haram da ake ta nema na tsawon wani lokaci.


Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Brigadier Sani Usman Kukasheka ya fadi cikin wata sanarwa cewa mutumin mai suna Aliyu Ahmed wanda aka fi sani da Aliko an kamashi da makamai a kauyen Yuga dake Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi inda yake buya.

A cewar Sojan Najeriya an same shi da bindiga babba da karama kuma ya amsa cewa akwai shi da bindiga  kirar AK-47 amma ta bace a lokacin da suka gwabza fada a bara.

Sojan Najeriya sun kuma sanar da kama wasu mutane hudu masu safarar yara kana a jihar Yobe domin an same su da yara  kanana 19.