rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ba zan lamunci rarrabuwar kai a gwamnatin Najeriya ba - Buhari

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa, kuma mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo a fadar gwamnati da ke birnin Abuja. REUTERS

Rahotanni sun ce shugaban Najeriya Muhd Buhari, yayi watsi da yunkurin wasu mukarraban gwamnatinsa, na ganin cewa ya sanya musu hannu kan wasu muhimman takardu ba ta hanyar tsallake mukaddashin shugaba, kuma mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.


Jaridar The Nation da ake wallafa ta a Najeriya, ta rawaito cewa, shugaba Buhari yaki bai wa mukarraban da suka tafi zuwa birnin London damar ganinsa, inda ya umarci da su mai dawa mukaddashin shugaban kasa farfesa Osinbajo muhimman takardun ya sa musu hannu a kai kamar yadda doka ta tanadar.

A cewar Buhari, ba zai lamunci duk wani yunkuri ba na haddasa rarrabuwar kai a gwamnatinsa.

Sai dai jaridar ta The Nation, ta rawaito cewar shugaba Buharin ya gana da mai dakinsa Aisha, a lokacin da ta kai masa ziyara a makon da ya gabata, ba kamar yadda wasu ke yadawa a shafukan dandalin sada zumunta be cewa, uwargidan shugaban kasar bata samu damar ganawa da maigidan nata ba.