rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mata 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutane 12 a Borno

media
Wani hari da kungiyar Boko Haram ta kai wa ayarin motocin dakon mai a garin Maiduguri kwanan baya STRINGER / AFP

A Najeriya wasu ‘yan mata biyar ‘yan kunar bakin wake sun tasar da bama-bamai inda suka kashe mutane 12 da jikkata wasu 11 a jihar Borno


‘Yan Sandan sun gaskata wadannan alkaluma inda suka ce suna ci gaba da gudanar da bincike sosai.

Babu wata kungiyar da ta fito fili ta ce ita ta tura ‘yan matan da jigidan bama-bama, amma kuma an saba ganin ‘yan kungiyar Boko Haram na wannan aiki.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan Borno Victor Isuku ya fadi cewa an kai wannan hari ne Lahadi da yamma a kauyen Kofa mai nisan kilomita takwas daga birnin Maiduguri.