Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Osinbajo zai gana da Sarakunan Arewa

A wannan Talata mukaddashin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, zai gana da sarakunan arewacin kasar, a kokarin kwantar da hankula dangane da sa-in-sar da ake yi tsakanin matasan arewaci da kudancin kasar, dangane da batun kafa kasar Biafra.

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.
Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo. citypeopleonline
Talla

A ranar lahadin da ta gabata, mukaddashin shugaban, ya gana da sarakunan kudu maso gabashin kasar kan wannan batu.

To sai dai a jiya Litinin kungiyoyin nan da suka fitar da gargadi ga ‘yan kabilar Igbo, tare basu wa’adin barin arewacin kasar kafin ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, sun bukaci Osinbajo, ya yi amafani da matsayinsa domin fara tsara yadda masu fafutukar kafa kasar Biafara za su fice daga Najeriyar kamar yadda suke so.

Cikin wasikar da kusoshin kungiyar matasan Arewan biyar suka sa wa hannu, sun yabawa kokarin mukkadashin shugaban, na tattaunawa da kowane bangare don warware takkadamar da ta kaure, sai dai sun ce, ba fa lallai bane ya samu nasarar hakan.

Yayin da yake Karin bayani, kan yadda za’a warware takaddamar ta fuskar doka, yayin tattaunawarsa da RFI Hausa, AbdulHameed Muhammad, Lauya mai zaman kansa da ke Abuja, ya ce babu wani tanadi da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada domin warware irin wannan matsala idan ta taso.

Don haka tilas a komawa majalisar kasa, domin a yiwa kundin tsarin mulkin kwaskwarima, ta yadda za’a iya sanya tsarin gudanarwa ko kuma kada kuri’ar raba gardama, da sauran sauye sauyen da ake da bukata.

02:55

Yadda za'a warware takaddamar kafa Biafra ta fuskan doka

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.