Isa ga babban shafi
Najeriya

Jamus ta gargadi Igbo kan fafutikar kafa kasar Biafra

Gwamnatin Kasar Jamus ta bukaci al’ummar Igbo da ke neman kafa kasar Biafra daga Najeriya da su mutunta kundin tsarin mulkin kasar domin ganin ta ci gaba da zama kasa guda.

Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel
Talla

Jakadan Jamus a Najeriya, Benhard Schlagheck, ya bayyana haka wajen wani taro da ya yi da shugabannin kabilar Igbo a Enugu, inda ya shaida musu cewar Gwamnatin Jamus na da yakinin cewar Najeriya na iya magance duk matsalolin da suka addabe ta.

Jakadan ya bukaci ‘yan kasar da su dinga tattauna matsalolin su tare domin ganin sun warware su maimakon bukatar raba kasa.

Shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo Chiedozie Ogbonnia ya ce bukatar tasu ta biyo bayan watsi da su da akayi wajen raba mukaman gwamnati, abinda yasa suka tashi tsaye domin samarwa mutanen yankin su matsayi mai kyau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.