Isa ga babban shafi
Najeriya

An kai jerin hare-hare a birnin Maiduguri

Wasu mutane da ake zaton mayakan Boko Haram ne, sun kaddamar da jerin hare-haren a wasu sansanonin ‘yan gudun hijira na Dalori da ke birnin Maiduguri a jihar Borno ta Najeriya.

Wasu 'yan gudun hijirar Boko Haram a wani sansani da ke birnin Maiduguri na Borno a Najeriya
Wasu 'yan gudun hijirar Boko Haram a wani sansani da ke birnin Maiduguri na Borno a Najeriya STRINGER / AFP
Talla

A cikin daren da ya gabata ne, mayakan suka kai hare-hare guda uku a sansanonin Dalori 1 da Dalori 2, yayin da aka kai hari na hudu da sanyin safiyar wannan rana ta Litinin.

Kawo yanzu dai, an tabbatar da mutuwar mutane hudu da kuma jikkatar 13 kamar yadda wani jami’i ya shaida.

Hare-haren na baya-bayan nan na zuwa ne kwanaki kalilan da shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanar Tukur Buratai ya bai wa kwamadan rundunar lafiya dole wa’adin kwanaki 40 da ya kamo Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.