Najeriya ta yi karin girma ga sojoji dubu 6
Rundunar sojin Najeriya ta yi wa sojoji dubu 6 da 199 karin girma sakamakon rawar da suka taka a yaki da kungiyar Boko Haram musamman a yankin arewa maso gabashin kasar, in da rikicin ya fi kazanta.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Sani Usman ya fitar, ta ce, shugaban sojin kasar, Laftanar Janar Tukur Buratai ya rattaba hannu don amince wa da karin girmar a wannan Talata.
Sanarwar ta ce, sojojin da aka yi wa karin girmar mabanbanta, na aiki ne a karkashin rundunar Operation Lafiya Dole.
Sanarwar ta bayyana adadin sojojin da sabbin mukamansu kamar haka haka:
1.Sitaf Saje -Warant Ofisa –329.
2. Saje -Sitaf Saje –371.
3. Kofur -Saje –707.
4. Las-Kofur – Kofur –1,290.
5. Firaivet – Las- kofur –3,502.
Rundunar sojin Najeriya ta bukaci sojojin da su kara kaimni wajen yaki da Boko Haram, wadda tun a shekarar 2009, sojojin ke fafutukar kawo karshenta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu