Isa ga babban shafi
Najeriya

Maharan bam sun mutu a Maiduguri

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wasu ‘yan kunar bakin wake uku da suka hada da mata biyu da na miji daya a birnin Maiduguri bayan sun yi yunkurin kaddamar da hari.

Jami'an 'yan sandan  Najeriya sun tabbatar da mutuwar 'yan kunar bakin wake a Maiduguri
Jami'an 'yan sandan Najeriya sun tabbatar da mutuwar 'yan kunar bakin wake a Maiduguri REUTERS/Stringe
Talla

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta ce, maharan sun yi kokarin kai farmakin ne a unguwar Usmanti da ke karamar hukumar Marafa da misalin karfe 9 da minti 49 na daren da ya gabata.

‘Yan kunar bakin waken sun tayar da bama-baman da suka yi damara da su bayan jami’an tsaro sun yi kokarin cafke su, yayin da biyu daga cikin jami’an tsaron suka samu rauni.

A yayin da hare-haren kungiyar Boko Haram ke neman sake tsananta a ‘yan kwanakin nan, rundunar sojin kasar ta bukaci jamian tsaro da su kara kaimi don ganin an murkushe mayakan kungiayar baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.