Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta lalata gidaje miliyan 1 a Borno

Gwamnatin jihar Barno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta bayyana cewa, kungiyar  Boko Haram ta lalata gidajen da suka kai miliyan guda da kuma azuzuwan makarantu 5,000 a fadin jihar.

Gidajen sansani 'yan gudun hijirar Boko Haram a Gambaru Nngala a Borno da ke Najeriya
Gidajen sansani 'yan gudun hijirar Boko Haram a Gambaru Nngala a Borno da ke Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Babban sakataren sake gina-gidajen da aka rusa, Yarima Saleh ya bayar da adadin ga manema labarai, in da ya ke cewa an yi asarar dukiyar da ta kai kusan tiriliyan biyu a rikicin na shekaru 6.

Alkaluman da jami’in ya bayar sun nuna cewa, kungiyar ta kona gidaje 986,453 da makarantu 5,335 da asibitoci 201 da gidajen samar da ruwan sha 1,630 da injinan samar da wutar lantarki 726.

Jami’in ya ce, ofisoshin jama’a da ofishin 'yan sanda da gidan yari 800 kungiyar ta lalata, abin da ya mayar da kananan hukumomi 22 daga cikin 27 wadanda ba za a iya aiki a cikin su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.