rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Likitocina ne suka hana ni komawa gida-Buhari

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP PHOTO / STRINGER

Shugaban Najeriya Muhd Buhari da ke jinya a birnin London, ya bayyana cewa, yana samun sauki sosai daga larurar da ya ke fama da ita kuma yana burin komawa gida amma likitocinsa ne ke ba shi umarni.


Shugaban ya  bayyana umarnin da likitocinsa ke ba shi a matsayin abin da ke ci gaba da tsare shi a London.

Buhari ya fadi haka a yayin da tawagar yada labaransa karkashin jagoranci ministan yada labarai da al’adu na kasar Lai Mohamed ta kai ma sa ziyara a yau Asabar.

Shugaba Buhari ya mika godiya ga 'yan Najeriya da sauran kasashen duniya bisa addu'oin samun lafiya da suke yi ma sa.

Sama da watanni uku kenan da Buhari ya koma London don ci gaba da duba lafiyarsa.