Biafra: Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tura karin jami'ai kudancin kasar
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kara yawan jami’anta a yankunan Kudu maso gabashi da kuma Kudu maso Kudancin kasar, domin murkushe duk wata barazanar tada zaune tsaye daga bangaren masu fafutukar neman kafa kasar Biafra, wadanda suka sha alwashin hana gudanar da zaben kujerar gwamnan Jihar Anambra.
Wallafawa ranar:
Zalika wasu majiyoyin daga hukumomin tsaron kasar, sun ce, rundunar ‘yan sandan na sanya idanu kan shugaban masu fafutukar ta kafa Biafra, wato Nmandi Kanu, domin dakile duk wani yunkuri da zai iya yi, na neman tserewa daga kasar, idan kotu ta amsa bukatar gwamnatin Najeriya, na janye belinsa, domin sake kama shi.
Gwamnatin Najeriya na zargin Nnamdi Kanu, da saba sharuddan da aka gindaya mishi na bada beli, kan haka ne kuma ta bukaci babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke belin, ta kuma bai wa jami’an tsaro damar sake damke shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu