Rundunar sojin Najeriya ta kare dalilin harbin gargadi a Umuahia
Rundunar sojin Najeriya tayi bayani kan dalilin da ya sa jami’anta suka yi harbin gargadi a garin Umuahia.
Wallafawa ranar:
Sanarwar sojin mai dauke da sanya hannun Manjo Oyegoke Gbadamosi, tace wasu matasa ne suka jefi tawagar sojojin dake ratsa garin, inda suka raunata soja guda da kuma wata mata dake wucewa, abinda ya sa sojojin suka yi harbin gargadi, amma babu wanda ya rasa rai.
Tun a makon jiya mazauna yankin kudu maso gabashin Najeriya ke korafi kan jibge sojojin.
Kamar yadda daya daga cikin mazauna jiohin da ke yankin Mazi Obinna Okparuba ya bayyana, yayinda yake zantawa da sashin Hausa na RFI, inda ya ce babu bukatar hakan tunda babu wani tashin hankali a yankin.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana dalilin harbin gargadi a Umuahia
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu