Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sanda sun koka bisa yawaitar aikata fyade a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta koka bisa yadda ta ce tana samun akalla rahoton aikata fyade, 10 zuwa 15 a kowace rana a sassan jihar.

Wasu daliban kasar India dauke da takardun kira da a kawo karshen aikata fyade a kasar da ma duniya baki daya a birnin New Delhi.
Wasu daliban kasar India dauke da takardun kira da a kawo karshen aikata fyade a kasar da ma duniya baki daya a birnin New Delhi. Reuters
Talla

Jumimah Ayuba, shugabar sashin yaki da laifukan cin zarafin dan’adam da aikata Fyade na osfishin ‘yan sanda da ke Shahuci, ta ce babban abinda ke cewa jami’an tsaron tuwo a kwarya, shi ne yadda a mafi akasarin lokuta, kananan yara manya ke yi wa fyaden.

Jumimah ta kara da cewa ba da jimawa bane suka fara kokarin gurfanar da wani magidanci da ya yiwa ‘ya’yansa uku fyade, zalika sun kame wani mutum da ya yiwa jaririya ‘yar watanni 2 kacal a duniya fyaden.

A cewar jami’ar ‘yan sandan bincikensu ya nuna cewa daga cikin manyan dalilan da ke haddasa yawaitar fyaden, akwai, tallace-tallace, rashin nuna kulawar iyaye zuwa ‘ya’yansu, daukar kananan yara a matsayin masu aiki a gidaje, da kuma yawaitar samun mutuwar aure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.