Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba za mu janye dakarunmu ba daga Abia- Rundunar Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta a karkashin shirin Operation Python Dance da aka kaddamar don magance miyagun ayyuka a yankin kudu maso gabashin kasar.

Babban Hafsn sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai
Babban Hafsn sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Rundunar ta bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da sanarwar da gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu ya fitar, wadda ke nuna cewa, za ta janye dakarunta da ake aiki a karkashin shirin Operation Python Dance II.

Mai Magana da yawun rundunar sojin, Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, ya ce, babu kamshin gaskiya a game da janye dakarunsu.

A ranar Alhamis da ta gabata ne, gwamna Ikpeazu ya ce, rundunar za ta fara janye sojojin daga titunan unguwannin jihar Abia a yau Jumma’a.

Za a ci gaba da gudanar da shirin har zuwa karshen shekara kamar yadda Sheka ya tabbatar.

Shirin ya kunshi yaki da masu garkuwa da mutane da fashi da makami da kashe-kashe da kuma yaki da miyagun ayyukan masu kokarin raba kan kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.