Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Kungiyar malaman Jami'o'i ta janye yajin aiki

Kungiyar Malaman Jami’oi ta Najeriya ta dakatar da yajin aikin da ta kira na sama da wata guda, inda ta bukaci malaman su koma aiki daga yau Talata.

kofar shiga Jami'ar Bayero University tsohuwar Makaranta.
kofar shiga Jami'ar Bayero University tsohuwar Makaranta. REUTERS/Stringer
Talla

Janye yajin aikin ya biyo bayan tarurrukan da aka dauki dogon lokaci ana yi tsakanin shugabannin lkungiyar malaman jami’oin da kuma tawagar gwamnati.

Ya zuwa yanzu dai babu cikkaken bayani kan batutuwan da bangarorin biyu suka amince da su a taron da suka yin a karshe.

A ranar 13 ga watan Agustan da ya gabata kungiyar ASUU ta shiga yajin aikin sai Baba ta gani, saboda rashin cika yarjejeniyar da gwamnatin Najeriyar ta yi, wadda suka cimma tsakaninsu a watan Nuwamba ne shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.