rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Lafiya WHO Maiduguri

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutum dubu 844 sun karbi rigakafin Kwalera a Najeriya-WHO

media
Sama da mutum dubu hudu aka tabbatar da cewa sun harbu da Kwalera a Borno REUTERS/Stringer

Hukumar Lafiya ta WHO, ta ce sama da Mutum dubu 844 ta yi wa rigakafin kariya daga cutar amai da gudawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda cutar da ta kashe akalla mutum 54.


Sama da mutum dubu hudu ne aka tabbatar da cewa sun harbu da cutar a wannan yanki mai fama da matsaloli sakamakon rikicin Boko Haram.

A ranar 16 ga watan Agusta aka samu bular cutar a Jihar Borno wadda tun daga wannan lokaci ya ke yaduwa akasari a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Kakakin WHO, Tarik Jasarevic, ya ce bayan rigakafin cutar da aka aiwatar, hukumar da sauran kungiyoyin agaji na taimakawa gwamnatin Najeriya wajen kafa cibiyoyin rigakafi na musamman a kauyuka.

Mista Jasarevic ya ce kwalare na yaduwa ne sakamaon gurbacewar ruwan sha.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Kusan Mutum miliyan 8 da rabi a arewacin Najeriya cikin miliyan 17 da ke zaune a yankunan Tafkin Chadi ke bukatar agajin gaggawa.