An kammala jigilar Alhazan Najeriya daga Saudiya
Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta kammala jigilar ‘yan kasar daga Saudiya da suka yi aikin hajjin bana.
Wallafawa ranar:
A wannan Litinin ne jirgin Max Airline mai lamba NGL 2110 ya kwaso tawagar karshe daga filin jiragen sama na King Abdulaziz da ke birnin Jeddah.
Jirgin wanda zai sauka a Kano bayan yada zango a birnin Fatakwal, ya taso daga Saudiya ne da misalin karfe 6:53 na safe agogon Najeriya.
NAHCON ta ce, akwai Alhazan Kano 172 da kuma Alhazan jihar Rivers 76 a cikin jirgin, sai kuma ma'aikata 30.
Tun a ranar 7 ga watan Satumban da ya gabata ne aka fara jigilar dawo da Alhazan Najeriya gida bayan kammala aikin hajjin bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu