rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An jibge Jami'an tsaro a Shalkwatar NNPC da ke Abuja

media
Karamin Ministan Man Fetur na Najeriya Emmanuel Ibe Kachikwu. Reuters

Rahotanni daga Abuja babban birnin Najeriya na cewa, an girke tarin jami’an tsaro da suka kunshi sojoji da ‘yansanda a Shalkwatar kamfanin man kasar NNPC da ke birnin a yau Asabar. Ana dai ganin hakan baya rasa nasaba da takaddamar da ta kunno kai tsakanin Ministan Albarkatun Man kasar Ibe Kachikwu da shugaban kamfanin na NNPC Mai Kanti Baru.


Sai dai a cewar wata majiya daga kamfanin, dama bisa al’ada akwai jami’an tsaron da dama da ke sanya ido a shige da ficen kamfanin kowacce rana, amma dai an kara yawansu a yau sakamakon bayanan da suka samu cewa akwai yiwuwar wasu taron matasa za su gudanar da Zanga-Zanga kan zargin da ake yiwa Shugaban na NNPC Mai Kanti Baru.

Tun da farko dai karamin Ministan albarkatun man fetur din Najeriyar Emmanuel Ibe Kachikwu ne ya aikewa shugaban kasar Muhammadu Buhari da wata takaddar Korafi, inda a ciki ya zargi Baru da cin amanar kasa, baya ga gudanar da wasu harkokin kamfanin da ya kunshi bayar da kwangila ba tare da sanin Mininstan ba.

Sai dai masu sharhi siyasa a kasar na kallon zargin a matsayin wani lamari da ka iya zama bi ta da kulli, ganin yadda shugaban ke tattaunawa kai tsaye da shugaban ba tare da sa hannun Ministan ba.

A jiya Juma'a ne dai Baru ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari a masallacin fadarsa ta Villa da ke Abuja jim kadan bayan idar da Sallar, sai dai babu cikakken bayanai kan ko sun tattauna dangane da takaddar korafin ko akasin haka.