rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cutar Karanbon biri ta watsu a wasu sassan Najeriya.

media
Cutar karanbon biri kenan da aka samu bullarta a wasu sassa na Najeriya, wadda masana kiwon lafiya suka yi ittifakin na samuwa ne sakamakon ta'ammali na naman biri. youtube

A Najeriya an kara samun bullar cutar Karanbon Biri da aka fi sani da MonkeyPox a turance, cikin jihar Akwa-Ibom da ke kudancin kasar a Lahadin nan. Wannan dai shi ne karo na biyu da aka samu sabon kamuwa da cutar tun bayan fara bullarta a jihar Bayelsa, duk dai a yankin kudancin kasar.


Mahukunta dai sun yi gargadin amfani da duk wani nau’in naman dawa ko mushe ko dabba mara lafiya don kare kai daga hadarin kamuwa da cutar.

Kawo yanzu dai ba a gano maganin cutar ba, yayinda a bangare guda kuma jami’an lafiya ke cewa akwai yiwuwar cutar na da saurin yaduwa.

Tuni dai Hukumar wayar da kai a Najeriyar ta fara fitar da bayanai dangane da yadda za a kare kai wanda ya kunshi batun tsaftace Muhalli da jiki dama abin da za a ci.