Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Alh. Mustafa Mai Kanuri kan rigar kariya ga gwamnonin Najeriya

Wallafawa ranar:

A Najeriya, wani batu da ake ci gaba da yin mahawara a kansa shi ne, rigar kariya da aka bai wa gwamnonin jihohi da mataimakansu, wadda ke hana a tuhume su a gaban kotu matukar dai suna rike da mukamansu. Wasu dai na ganin cewa matukar ba wannan rigar kariya, to zai kasance abu mai wuya gwamna ko mataimakinsa ya iya tafiyar da mukaminsa, yayin da wasu ke zargin cewa, wadannan mutane na amfani da damar domin aikata laifi, amma kuma ba za a iya gurfanar da su a gaban kuliya ba. A zantawarsa da AbdoulKarim Ibrahim Shikal, Alhaji Muhammad Mustapha Maikanuri, na da ra’ayin cewa cire rigar kariyar, shi ne babban abin da shugaba Buhari zai yi wa ‘yan Najeriya da ba za su taba mantawa da shi ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.