Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya gana da gwamnonin arewa kan sha'anin tsaro

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana a kebe da wasu gwamnonin jihohin arewa a jiya Litinin, in da suka tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro da kuma gano man fetir a yankin arewan kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP
Talla

Gwamnonin da Buhari ya gana da su a fadarsa da ke birnin Abuja, sun hada da Ibrahim Gaidam na Yobe da Aminu Tambuwal na Sokkoto da kuma Abubakar Badaru na Jigawa.

Bayan kammala ganawar, gwamna Tambuwal ya shaida wa manema labarai cewa, ya sanar da shugaba Buhari game da sakamakon ziyarar da wasu gwamnonin arewa suka kai yankin kudu maso gabashin kasar saboda fafutukar da wasu ke yi ta neman raba kasar.

Tambuwal ya ce, sun tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da halin da harkar tsaro ke ciki a sassan Najeriya.

Tambuwal ya kara da cewa, sun yi amfani da damar ganawar wajen sanar da shugaba Buhari kan yiwuwar gano man fetir a jihar Sokkoto.

A cewar Tambuwal, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta ci gaba da agazawa dangane da kokarin gano man fetir a yankin, abin da gwamnan ya ce, zai taimaka wajen kara yawan mai da iskar gas da Najeriya ke samarwa.

Shi kuwa a nashi bangaren, Ibrahim Gaidan cewa ya yi, ya shaida wa Buhari cewa, an samu zaman lafiya a Yobe, daya daga cikin johohin da ke fama da rikicin Boko Haram.

Gaidam ya kuma shaida wa Buhari cewa, mutanen da rikicin ya raba da muhallansu sun koma matsugunansu kuma a halin yanzu sun ci gaba da sana’oinsu.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau News Ghana

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.