rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari Rashawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari ya kori Babachir Lawal

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kori sakataren gwamnatin tarayyar Babachir Lawal inda ya maye gurbinsa da Boss Mustapha.


Sanarwar da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yadda labarai Femi Adesina ya fitar, ta ce shugaban ya dau wannan matakin ne bayan gamusawa da rahotanni kwamiti na musamman da aka kafa domin bincike karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa ferfesa Yemi Osinbajo.

Kazalika shugaban ya kuma kori shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA Ambassador Ayo Oke.

A cewar sanarwar shugaba Buhari ya kuma amince da kafa kwamiti mutane 3 da zai nazarci yadda aka gudanar da ayyuka da kuma gyaran da ake bukata a hukumar NIA.

An ji ma dai ana zargin manyan jami’an gwamnatin da almundahana, ko da dai sun sha musantawa.