Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta yi watsi da bukatar Jonathan

Wata Kotu da ke Najeriya ta yi watsi da bukatar tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan cewar sai a bashi naira biliyan guda kafin ya je ba da shaida kan shari’ar cin hanci da rashawa da ake yiwa tsohon kakakin PDP Olisa Metuh.

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Alkalin Kotun Okon Abang ya ce babu dalilin da tsohon shugaban zai bukaci ba shi wadannan makudan kudaden a matsayin wadanda zai dinga amfani da su wajen tafiya Abuja domin ba da shaida.

Alkalin Obang ya kuma ki amincewa da bukatar lauyan tsohon shugaban na janye wa’adin sammacin gayyatar tsohon shugaban domin bada shaida.

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da Metuh kan zarginsa da hannu a badakalar kudaden da yawansu ya kai Naira milyan 400 daga kudaden makamai na hannun tsohon mai bai wa shugaban shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki.

Mista Metuh ya ce dole sai an gabatar da Jonathan gaban kotun domin warware zare da abawa a kan batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.