Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan wasan Super Eagles sun isa Marocco

'Yan wasan kwallon kafar Najeriya, Super Eagles da ke taka leda a kungiyoyin kwallon kafar duniya daban-daban sun fara hallara a Morocco gabanin wasan da kasar za ta fafata da Algeria duk dai cikin shirye-shiryen tunkarar wasannin cin kofin duniya na shekarar 2018 da zai gudana a Rasha.

Tuni dai hukumar kwallon kafar Najeriyar ta gayyato 'yan wasan kasar daban-daban da ke taka leda a kasashen Duniya don dafa mata a gasar cin kofin duniyar da zai gudana a Rasha badi.
Tuni dai hukumar kwallon kafar Najeriyar ta gayyato 'yan wasan kasar daban-daban da ke taka leda a kasashen Duniya don dafa mata a gasar cin kofin duniyar da zai gudana a Rasha badi. AFP/Javier Soriano
Talla

A yau ne Captin din Super Eagle Mikel Obi da mai tsaron ragar kungiyar Francis Uzoho da kuma Daniel Akpeyi suka isa Rabat a Morocco, yayinda tun a jiya litinin tarin ‘yan wasa da suka hadar da Oghenekaro Etebo da Alex Iwobi da Henry Onyekuru da kuma Chidiebere Nwakali da Kelechi Iheanacho da Uche Agbo da Chidozie Awaziem tare da John Ogu da kuma Anthony Nwakaeme suka isa kasar ta Marocco.

Haka zalika rahotanni sun ce tun a ranar Lahadi ne Ahmed Musa da Wilfred Ndidi da Ikechukwu Ezenwa suka hallara a Maroccon.

A cewar Amaju Pinnic har yanzu Victor Moses bai samu cikakkiyar Lafiyar da zai taka leda a wasannin da Najeriyar za ta buga ba, haka kuma an gayyato ‘yan wasan kasar da ke taka leda a kasashe daban-daban don bayar da ta su gudunmawar a wasannin yanzu da ma wadanda kasar za ta yi a gasar cin kofin duniya badi.

Tuni dai Najeriyar ta samu gurbi a gasar cin kofin duniyar, kuma ita ce kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta samu gurbin, yayin da yanzu haka ta ke take sahun gaba a rukunin B.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.