Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya bayyana dalilin da ya haifar da tsaiko ga aiwatar da kasafin 2017

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya soke damar daukar sabbin ma’aikata da dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin kasar da ita a baya, har sai sun samu amincewar ofishinsa kai tsaye.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin gabatart da kasafin kudi a zauren hadaka na majalisun kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin gabatart da kasafin kudi a zauren hadaka na majalisun kasar. Nigeria Presidency/Handout via REUTERS.
Talla

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayinda yake gabatar da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2018 mai kamawa a gaban zauren hadaka na ‘yan majalisar dattijai da na wakilan kasar, a garin Abuja, inda ya shafe kimanin Sa’a daya da rabi yana bayani.

A cewar shugaban matakin zai saukakawa gwamnati wajen kyautata amfani da kudade a kan ka’ida wajen tafiyar da ayyuka da albashi ba tare da ab rika samun gibi ba. Hakan kuma zai kara taimakawa, wajen bin ka’idojin da yakamata, yayin daukar sabbin ma’aikata.

Kasafin kudin shekarar ta 2018 ya kai tiriliyan 8.6, sabanin na shekarar 2017 da aka yi kan tiriliyan 7.4.

Yayinda yake Karin haske kan halin da ake cikin dangane da aiwatar da kasafin kudin wannan shekara, shugaba Buhari ya ce zuwa karshen watan Oktoba, gwamnatinsa ta fitar da naira biliyan 450, daga cikin tiriliyan 2.2, da aka ware domin gudanar da manyan ayyuka a kasar.

A cewarsa zuwa karshen watan Disamba mai zuwa gwamnatinsa zata cimma burin aiwatar da kashi 50 na kasafin kudin shekarar 2017.

Muhammadu Buhari, ya dora alhakin tsaikon da aka samu wajen aiwatar da kaso mafi yawa na kasafin kudin na 2017 a kan, rashin amincewa da kasafin a kan lokaci da ‘yan majalisun suka yi, wanda ya jawo rashin fitar da kudaden da ake bukata a kan lokaci.

Naira tiriliyan 3.5 daga cikin kasafin na tiriliyan 8.6, za’a yi amfani da su ne wajen gudanar da ayyuka na

yau da kullum, yayinda aka warewa manyan ayyuka naira triliyan 2.7.

A bangaren biyan wani yanki na bashin da ake bin Najeriya kuwa, Muhammad Buhari ya ce za’a yi amfani da naira tiriliyan 2.

Dangane da farashin gangar danyen mai da aka kafa turakun kasafin kudin kuwa, shugaban ya ce an dora shi ne bisa dala 45 kan kowacce ganagar danyen man, sabanin dala 44 kan kowace ganga da aka gina kasafin kudin shekara ta 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.