Isa ga babban shafi
Najeriya

Plateau - Ana zaman zullumi a Riyom

Mai Magana da yawun gwamnan jihar Filato Dan Manjang ya ce mutane na zaman zullumi a yankin da aka kai harin

An sha kai hare-hare a kauyukan jihar filato
An sha kai hare-hare a kauyukan jihar filato Reuters/Carmen McCain
Talla

Manjang ya ce daga cikin matasan yankin wasu sun yi kokarin yin zanga-zanga, amma an shawo kan su.

A cewarsa, mutane sun fara zargin jami’an tsaro da hannu a cikin kashe-kashen da ake yi a yankin, domin har zuwa yanzu an kasa kama wadanda ke kawo wadannan hare-hare.

Amma jami’in ya ce yana iya yiwuwa rikicin na da nasaba da siyasa, musamman ganin cewa zaben kananan hukumomi ya karato.

Rahotanni daga jihar ta Filato sun ce akalla mutane 9 aka tabbatar da mutuwar su lokacin da wasu yan bindiga suka kai hari a karamar hukumar Riyom lokacin mutane ke komawa gida bayan sun ci kasuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.