Najeriya ta sa hannu kan Kwangilar gina tashar lantarki a Mambilla
Gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan kwangilar fara aikin gina tashar samar wutar lantarki ta Mambilla da ke jihar Taraba, wadda zata samar karfin wutar megawatts dubu 3,050, bayan shafe shekaru akalla 40 ana kokarin tabbatar da shirin.
Wallafawa ranar:
A ranar Juma’ar da ta gabata ne Ministan bunkasa makamshi, ayyuka da samar da gidaje na Najeriya Baba Tunde Fashola, ya sanya hannu kan takardar yarjejeniyar fara aikin hadin gwiwar da wasu kamfanonin kasar China.
Ginin tashar lantarkin da za’a shafe shekaru 6 kafin kammala shi, zai lashe dala biliyan 5 da miliyan 800, wato naira triliyan 2.1 kenan.
Bankin Exim na China ne zai samar da dala biliyan 4.9 yayinda gwamnatin Najeriya zata bada kashi 15, wato dala miliyan 868.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu