Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari - Ba za mu amince da bara-gurbin malamai ba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu wata kasa da za ta cigaba a duniya ba tare da koyarwar kwararru kuma gogaggun malamai ba.

Yanzu haka ana takaddama a Najeriya kan aniyar gwamnan jihar Kaduna na korar malaman firamare.
Yanzu haka ana takaddama a Najeriya kan aniyar gwamnan jihar Kaduna na korar malaman firamare. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Buhari ya fadi haka ne a wurin taron bita kan matsalaolin da harkar ilimi ke fuskata, wanda aka shirya ma wakilan majalisar zartarwar kasar, a Abuja, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta amince malamai bara-gurbi su cigaba da koyarwa a makarantun kasar ba.

Ya ce abin takaici ne a ce malamai sun kasa cin jarabawar da yaran da suke koyarwa suke rubutawa ba.

A cewarsa gwamnati za ta yi duk abinda ya kamata wajen ganin ta kawo gyara a fannin na ilimi domin samun cigaban da ya dace.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.