Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan fashi sun kashe mutane 45 a Zamfara

Wasu ‘yan fashi sun kashe mutane kimanin 45 a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara a taraayyar Najeriya.

Ana yawan zargin makiyaya da kai jerin hare-hare a jihar Zamfara ta Najeriya
Ana yawan zargin makiyaya da kai jerin hare-hare a jihar Zamfara ta Najeriya shakarasquare
Talla

Dr. Sulaiman Shu’aibu Shinkafi na kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ya shaida wa sashen hausa na rfi cewa, daga cikin wadanda ‘yan bindigan suka kashe har da matan da maharan suka yi wa yankar rago a kauye Tunga-Kaho kafin daga bisani su cinna wa garin wuta.

Maharan sun kai farmaki na biyu a kauyen Mallamawa, in da anan ma suka kashe maza da mata.

Dr. Shuaibu ya zargi gwamnatin jihar da yin sakaci wajen magance matsalar hare-hare kan jama’a a jihar Zamfara, in da ya ce, ba a karon farko kenan ba da ake kai irin wannan kazamin harin amma har yanzu an gaza kawo kasrshen sa.

Yanzu haka akwai mutanen da ke ci gaba da samun kulawa a babban asibitin Shinkafi sakamakon raunin da suka samu a sanadiyar harin na daren jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.