Isa ga babban shafi
Najeriya

Jam'iyyar APGA ta lashe zaben jihar Anambra

Dan takarar Jam’iyyar APGA, Willie Obiano, ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra da ke kudancin Najeriya.

Gwamnan jihar Anambra Willie Obiano, wanda ya sake lashe zaben kujerar gwamnan jihar.
Gwamnan jihar Anambra Willie Obiano, wanda ya sake lashe zaben kujerar gwamnan jihar. Pulse.ng
Talla

Sakamakon zaben ya nuna cewa, Mista Obiano, shi ne kan gaba, wajen lashe kuri’un da aka kada a baki dayan, kananan hukumomi 21 da ke jihar, inda ya samu kuri’u dubu 234.

Dan takarar jam’iyya mai mulki ta APC, Tony nwoye ne ya zo na biyu, yayinda Oseloka Obaze na jam’iyyar PDP, ke biye masa a matsayi na uku.

Zaben gwamnan jihar ta Anambra, ya kafa tarihin zama wanda aka fi samun yawan ‘yan takara a cikinsa, inda mutane 37 suka fafata, a zaben na ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.