Isa ga babban shafi
Najeriya

Atiku Abubakar zai karbi katin komawa PDP

A yau Lahadi ne ake sa ran tsohon mataimakin sugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar da ya sauya sheka daga jam’iyya mai mulkin kasar zai karbi katinsa na komawa tsohuwar Jam’iyyarsa ta PDP da ta sha kaye a zaben shekarar 2015.

Kafin yanzu dai, Atiku Abubakar ya fara siyasa ne karkashin jam’iyyar PDP daga bisani ya sauya sheka zuwa APC ya kuma karo dawowa PDP kafin komawarsa APC.
Kafin yanzu dai, Atiku Abubakar ya fara siyasa ne karkashin jam’iyyar PDP daga bisani ya sauya sheka zuwa APC ya kuma karo dawowa PDP kafin komawarsa APC. Reuters
Talla

Wani na hannun daman tsohon mataimakin shugaban kasar, Ahmed Lawan, kuma sakataren gudanarwa Jam’iyyar APC mai mulki ya shaidawa kafofin labaran kasar cewa za ayi rijistar Atiku Abubakar yau a ofishin jam’iyyar PDP da ke mazabar Jada da ke garin Yolan jihar Adamawa.

Kafin yanzu dai, Atiku Abubakar ya fara siyasa ne karkashin jam’iyyar PDP daga bisani ya sauya sheka zuwa APC ya kuma karo dawowa PDP kafin komawarsa APC a shekarar 2014.

Sai dai a cewar, Ahmed Lawan ya gargadi tsohon mataimakin shugaban Najeriyar kan ya yi karatun ta nutsu kafin aikata abin da yake shirin yi kasancewar ficewarsa daga jam’iyyar ta APC ka iya zama karshen siyasarsa a kasar.

Ya kuma bukaci Atiku Abubakar ya tuna kalaman da ya furta bayan shigarsa Jam’iyyar APC cewa ‘‘idan akwai wani abu da zai iya sanya shi fita daga jam’iyyar APC to kuwa hakan zai zama lokacin murabus dinsa a siyasa’’.

A cewar Ahmed Lawal babu gaskiya cikin batun da ke cewa ana nunawa tsohon mataimakin shugaban kasar bambanci karkashin jam’iyyar APC kawai dai ya ga babu yiwuwar ya iya yin nasara kan shugaban kasar Muhammadu Buhari idan aka zo batun zaben fidda gwani a takarar shugabancin kasar na 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.