Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Borno za ta mayar da fadar shugaban Boko Haram gidan Tarihi

Gwamnatin Jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya na shirye-shiryen mayar da gidan tsohon jagoran kungiyar Boko-Haram Muhammad Yusuf zuwa gidan tarihi. Matukar shirin ya kammala a kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar zai taimaka gaya wajen samar da kudaden shiga baya ga kasancewa Izina da kuma ga wadanda za su taso nan gaba.

Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima.
Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima. via thisday
Talla

A cewar kwamishinan al’adu da adana kayakin tarihi na jihar, Dr Muhammad Bulama, lokacin da yak e zantawa da manema labarai yayin wani taron hukumar kula da al’adu da ‘yan yawon bude ido da ya gudana a birnin Dutsen jihar Jigawa, hakan zai taimakawa yaran da za su taso a nan gaba sanin irin banner da kungiyar ta Boko Haram ta Tafka a Najeriya.

Dr Muhammad Bulama ya ce za kuma su yi kokarin tattara duk wasu kayakin kungiyar da suka kama wajen tara su a gidan ta yadda za a rika bayar da dama don shiga a gansu a nan gaba kadan.

Taron dai ya mayar da hankali kan yadda za a bunkasa harkokin yawon bude ido a kasar da nufin farfadowa tare da baza komar tattalin arziki.

Gwamnatin ta Borno, ta ce za ta sake gina wurin wanda ake kira da suna Markaz don janyo hankalin ‘yan yawon bude ido daga sassan duniya daban-daban dama masu son sanin irin barnar da mayakan na kungiyar Boko Haram suka aikata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.