Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun 'yanto mutane 212 daga Boko Haram

Sojojin Najeriya da suka kaddamar da aikin kakkabe sauran mayakan Boko Haram a wasu kauyuka da ke jihar Borno ta Najeriya, sun ‘yanto mutane 212 da hannun ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su.

Sojin Najeriya da ke yaki da 'yan Boko Haram a Borno
Sojin Najeriya da ke yaki da 'yan Boko Haram a Borno Photo: Stefan Heunis
Talla

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin kasar, Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ya fitar ta ce, sojojin sun kuma yi nasarar cafke daya daga cikin Kwamandojin Boko Haram, Amman Judee, baya ga ‘yan ta’adda hudu da suka kashe.

Kuka Sheka ya ce, a ahalin yanzu ana kan gudanar da bincike kan Kwamandan na Boko Haram, yayin da tuni aka dauki bayanan mutanen da aka ceto.

A karo na biyu kenan a cikin wannan makon da sojin Najeriya ke ‘yanto wani adadi mai yawa na mutane daga hannun Boko Haram.

Kimanin mutane dubu 100 ne suka rasa rayukansu tun lokacin da rikicin Boko Haram ya yi kamari a shekarar 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.