Isa ga babban shafi
Najeriya

Za mu kwaso 'yan Najeriya daga Libya-Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kwaso daukacin yan Najeriya da suka makale a kasar Libya, inda yanzu haka ake sayar da baki bakaken fata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Matsalar cin zarafi tare da sayar da bakaken fata kamar bayi, musamman masu bi ta kasar Libya domin tsallakawa zuwa kasashen Turai na daga cikin abubuwan da suka dauki hankalin al'ummar duniya.

Yayin ganawa da 'yan Najeriya mazauna Abidjan, inda ya ke halartar taron shugabannin kasashen nahiyar Afirka da Turai, shugaba Buhari ya ce a matsayinsa na shugaban daukacin 'yan Najeriya yana gudanar da aikinsa ba tare da nuna banbanci ba kamar yadda ya bayyana ranar da ya dauki rantsuwa.

A baya, sakatare-janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bukaci kasashen duniya da su yunkuro domin kawo karshen al'amarin.

Kwararan 'yangudun hijira daga kasashen Afirka zuwa Turai na daya daga cikin abubuwan da ake sa ran shugabannin kasashen nahiyar Afirka da Turai za su tattauna a kai, a taron da yanzu haka ke gudana a kasar ta Cote d'Ivore.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.