rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Libya Bakin-haure Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya ta kwaso bakin-haure 1, 295 daga Libya cikin Nuwamba

media
Wasu bakin haure da ke tsare a sansanin Gharyan a kasar Libya. REUTERS/Hani Amara

Wani kashi na bakin-haure ‘yan Najeriya da suka makale a Libya, da yawansu ya kai 152 sun isa gida, kawanaki kadan bayan dawowar wasu 242.


Tun bayan alkawarin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi, na kwashe baki dayan ‘yan Najeriya da suka makale a Libya, aka matsa kaimin tabbatar da kwaso 'yan kasar daga kasar ta Libya.

Hakan ya sa zuwa yanzu ‘yan Najeriya da suka makale a Libya dubu 1, 295 ne aka kwashe zuwa gida cikin watan Nuwamba da ya gabata.

Har yanzu duniya na ci gaba da yin alla wadai, da yadda cinikin bayi ya samu gindin zama a Libya, da kuma yadda wasu ‘yan kasar ke cin zarafin bakin-hauren da suka yi yunkurin tsallakawa zuwa nahiyar turai.