Isa ga babban shafi
Najeriya

Atiku ya fahimci akwai karya a jam'iyyar APC- PDP

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana cewa, matakin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Abubakar Atiku ya dauka na raba gari da APC, wata alama ce da ke nuna cewa, ya fahimci karerayin da ke kunshe a APC mai mulki.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Wata sanarwa da sakataren watsa labaran jam’iyyar ya fitar, Prince Dayo Adeleye ta ce, PDP gida ne ga Atiku kuma tana kira ga sauran wadanda suka raba gari da ita a can baya da su dawo gida.

Sanarwar ta kara da cewa, “PDP na marhaba da dawowar tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Abubakar Atiku ( Wazirin Adamawa)”.

Atiku ya bayyana cewa, APC ta gaza wajen aiwatar da manufofin da suka janyo hankalinsa har ya raba gari da PDP.

00:41

Muryar Atiku Abubakar kan hujjarsa ta komawa PDP

Daga cikin manufofin akwai batun samarwa da matasa miliyan uku aiki a kowacce shekara amma APC ba ta cika alkawarin ba kamar yadda Atiku ya bayyana.

PDP ta bayyana dawowar Atiku a matsayin gagarumar nasara dangane da kokarinta na magance matsalolin da jam’iyyar ke fama da su kafin gudanar da zaben 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.