Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP na neman afuwar 'yan Najeriya- Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana Jam’iyyar PDP a matsayin sabuwa, in da ya bukaci ‘yan Najeriya su yi mu su afuwa kan kura-kuran da suka tafka a matsayinsu na ‘yan Adam.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

A yayin zantawarsa da sashen Hausa na RFI, Atiku wanda ya koma PDP a ‘yan kwanakin da suka gabata bayan ya raba gari da APC mai mulki ya ce, sun kama hanyar kawo gyara a PDP bayan zaben sabbin shugabannin jam'iyyar a karshen mako.

01:05

Muryar Abubakar Atiku kan neman afuwar 'yan Najeriya

A wani sako da ya aike ta kafar twitter, Atiku ya ce lokaci ya yi da ya kamata PDP ta hada kai don ganin cewa ta karbe ragamar tafiyar da Najeriya.

Atiku Abubakar tare da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a wurin taron jam'iyyar PDP

A shekarar 2015 ne jam’iyyar APC ta kwace mulki daga hanun PDP wadda ta yi mulki tsawon shekaru 16 bayan karawar da aka yi tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.