Isa ga babban shafi
Najeriya

"Rashin adalci ne a tilasta wa Buhari kan rahoton 2014"

Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya, Abdullahi Adamu ya ce, rashin adalci ne a yi dakon shugaban kasar Muhammadu Buhari wajen aiwatar da shawarwarin da aka tattara a rahoton taron hadin-kan-ƙasa da aka gudanar lokacin mulkin Goodluck Jonathan a shekarar 2014.

Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS
Talla

Adamu ya bayyana haka ne gabanin bude taron Ƙungiyar Sanatocin da yanzu haka ke gudana a jihar Katina da ke arewacin kasar don tattaunawa kan matsalolin da suka hada addabi arewa da kasar baki daya.

A cewar Adamu, babu yadda za a tilasta wa Buhari aiwatar da rahoton da aka fitar bayan taron hadin-kan-ƙasar, musamman ma idan aka yi la’akari cewa, shugaban ba shi da hannu a rahoton.

Taron na yau wanda ya samu halartar Sarakunan gargajiya, zai kuma tattauna kan fafutukar sake fasalta Najeriya da kuma batun kasafin kudi baya ga matsalar tsaro a wani sashi na arewacin kasar.

Sanatoci 58 ne daga shiyoyin arewa uku ke halartar taron na yau.

Kazalika gwamnonin jihohin Kebbi da Zamfara da Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar da wasu daga cikin manyan mutane sun halarci taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.