Isa ga babban shafi
Najeriya

Wani hari ya kashe mutane a jihar Borno

Wani harin ƙunar baƙin wake a Pulka da ke Jihar Bornon Najeriya ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 4, yayin da sojojin Najeriya biyu suka mutu bayan da motarsu ta taka nakiya a gefen hanya.

Sojojin Najeriya sun sha alwashin kammala yaki da Boko Haram
Sojojin Najeriya sun sha alwashin kammala yaki da Boko Haram REUTERS/Tim Cocks
Talla

Kakakin rundunar da ke yaki da Boko Haram, Kanar Onyema Nwachukwu ya ce, wasu yan mata biyu ne suka kai harin kunar bakin waken da ya hallaka mutanen 4, in da suka harbe guda bayan dayan ta tada bam din da ke jikinta.

A zantawarsa da sashen hausa na RFI, sabon kwamandan rundunar Zaman Lafiya Dole, Janar Nicholas Rogers ya sha alwashin kammala yaki da Boko Haram bayan da ya karbi ragamar tafiyar da rundunar.

00:55

Muryar Janar Nicholas Rogers kan Boko Haram

Janar Rogers ya bukaci jama’a da su taimaka mu su wajen musayar bayanan da za su kai ka nasarar murkushe ‘yan ta’adda cikin gaggawa.

Janar Roger ya ce, ƴan ta’addan na da damar mika wuya ga hukumomin tsaron kasar, in da ya ce, za su killace wadanda suka mika kansu a wani wuri na musamman.

Mayakan Boko Haram dai sun hallaka mutane da dama musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.