Sojin Najeriya sun kame mayakan Boko Haram 167
Jami’an sojin Najeriya da ke karkashin rundunar musamman ta Operation Lafiya Dole, sun samu nasarar kame mayakan Boko Haram, 167.
Wallafawa ranar:
Cikin sanarwar da ya sa wa hannu, Kanal Onyema Nwachukwu, mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar ta musamman, ya ce an samu nasarar ce, bayan sabunta kai wa mayakan na Boko Haram farmaki a yankunan da ke zagaye da tafkin Chadi, makwanni 2 da suka gabata zuwa yanzu.
Sojin Najeriyar sun kuma ceto mata 67, da yara 173 daga hannun mayakan.
Wani lokaci nan gaba ake sa ran mika fararen hular zuwa hukumomin da ke lura da sansanonin ‘yan gudun hijira da ke arewa maso gabashin kasar, bayan an kammala tantance su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu