rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Italiya Shari'a Najeriya Rashawa Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun Italiya ta bukaci gurfanar da kamfanonin Eni da Shell

media
Shell REUTERS/Benoit Tessier/File Photo

Wata Kotu a kasar Italiya ta bukaci gurfanar da manyan kamfanonin hako man Eni da Shell saboda samun su da hannu wajen bada cin hanci ga jami’an gwamnatin Najeriya dangane da cinikin wata rijiyar mai da aka yi cinikin ta akan Dala biliyan 1 da miliyan 300.


Cikin wadanda ake zargi da karbar na goro a shari’ar harda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da ministan shari’ar sa Bello Adoke da kuma tsohon ministan man fetur Dan Etete, amma duk sun yi watsi da zargin.

Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu daga cikin jami’an a gaban kotu amma har yanzu shari’ar bata kare ba.

Kamfanonin dai sun jajirce a kan cewa sun gurfanar da ayyukansu a Najeriya bisa tsari da doka.